Saudi Arebiya za ta fara bada bizar aikin Hajjin baɗi a watan Fabrairun 2025

0
177

Ƙasar Saudiyya ta sanar da cewa za a fara bayar da biza ga maniyyata aikin Hajjin baɗi daga ranar 19 ga watan Fabrairun 2025.

An bayar da wannan sanarwar ne a yayin wani taron kammala aikin hajjin bana na 2024.

Saudiyya ta bayyana cewa za a fara jigilar maniyyatan badi a watan Afrilun 2025.

Sanarwar da Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta fitar ta bayyana cewa Saudiyya ta sanya ranar 4 ga Satumba, 2024, don fara taron share fagen shirye-shiryen aikin Hajjin baɗi da kamfanunuwan hidimar aikin Hajjin badi.

A halin da ake ciki, Shugaban Hukumar NAHCON, Jalal Arabi, ya ce Najeriya za ta ci gaba da karbar kason kujerun aikin Hajji na dubu 95,000 na aikin Hajji na shekarar 2025.