Abin da da yawana mutane ba su ne ba shi ne, kusa dukkanin kayan abincin gargajiyar da aka yi amfani da su wajen shirya wa alhazan Najeriya abinci yayin aikin Hajjin bana a Saudiyya ƙaƙashin inuwar Ithraa Alkhair, ƙoƙarin Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ne.
Wani ma’aikacin kamfanin Ithraa Alkhair ya shaida wa HAJJ REPORTERS cewar, dukkanin ƙoƙarin da kamfanin ya yi wajen tabbatar da alhazan Najeriya sun samu abincin gida, ya yi hakan ne bisa umarnin NAHCON.
Ya ce, “mun yi jigilar kayan abinci daban-daban sama da buhu 5000 daga Najeriya domin tabbatar da alhazan Najeriya sun samu abincinsu na gargajiya yayin aikin Hajjin bana kamar yadda NAHCON ta ba da umarni.
“Kuma bayan da muka tanadi kayan abinci, NAHCON ta ba da gagarumar gudunmawa wajen tabbatar da an kwashe kayan zuwa Saudiyya a kan lokaci.”
Jami’in ya ƙara da cewa, sayen kayan abincin daga Najeriya ya taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin waɗanda suka yi aikin samar da abincin.
A cewarsa, wannan shi ne burin Shugaban kamfanin Mutawif, Dr Ahmed Sindi, kamfanin da ke kula da alhazan ƙasashen Afirka da ba Larabarawa ba.
Bugu-da-ƙari, an rawaito Ithraa Alkhair ya ɗauki ma’aikata kimanin 50 daga Najeriya wanda a yanzu haka suna aiki a kamfanin a sashen sarrafa abinci a Makka. Wannan wata dama ce ta kyautata rayuwar ma’aikatan da na ‘yan uwansu.
Haka nan, ya ce, “Mun ɗauki hayar masana ingancin abinci daga Najeriya waɗanda suke aiki a sashen dafa abinci don cim ma buƙatun alhazan Najeriya kulli yaumi.
“NAHCON ta buƙaci mu samar da abincin gargajiya ga alhazan Najeriya, inda Shugaban kamfanin Ithraa Alkhair ya yi alƙawarin yin dukkanin mai yiwuwa wajen gamsar da baƙin Al Rahman,” in ji shi.
Kazalika, ya ce, Dr Sindi da kansa ya sanya ido kan yadda aka yi jigilar kayan abincin daga Najeriya zuwa Saudiyya don tabbatar da an cim ma tsarin da NAHCON ta gindaya.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa a wannan karon ba a samu ƙorafe-ƙorafe ba game da ɗanɗanon abinci.
Idan dai za a iya tunawa, a baya NAHCON ta yi alƙawarin cewa, yayin Hajjin bana za a ciyar da alhazan Najeriya da irin abincinsu na gargajiya a lokacin zamansu a Saudiyya.
Sakamakon bibiyar lamarin da HAJJ REPORTERS suke yi, sun gano cewa hukumar Hajji ta ba da umarnin a tabbatar da kamfanin da aka bai wa aikin kula da abincin alhazan Najeriya ya tanadar wa alhazan irin nau’in abinci da suke buƙata.