Hajji 2024: Gwamna Raɗɗa ya bai wa alhazan Katsina Goron Sallah

0
77

Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa phD, ta kashe fiye da Riyal milyan ɗaya a matsayin goron sallah ga alhazan Jihar Katsina.

Wannan ya biyo bayan alƙawarin da Gwamnan ya ɗauka na tallafa wa alhazai, musamman a wannan lokacin da kowane alhaji ya kammala aikin Hajji yana dakon a maido shi gida.

Wasu daga cikin alhazan da lamarin ya shafa sun ce, wannan karamcin da Gwamna ya yi musu ya taimaka musu ainun kasancewar ihsanin ya zo a daidai lokacin da kuɗin guzirin galibin alhazan ya ƙare.

Wannan ba shi ne karon farko da gwamnatin jihar ke aiwatar da irin wannan abin a yaban ba ga alhazan jihar.