Samun tanti-tanti a kusa da wajen jifan shaiɗan zai ƙara kuɗin aikin Hajji, NAHCON ta gargaɗi ƴan Nijeriya

0
138

Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta ce maniyyata za su biya maƙudan kuɗaɗe na aikin Hajji in dai suna son zama a tanti-tanti da ke kusa da Jamrat, wajen jifan shaiɗan.

Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Arabi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar Hukumar da ke Makkah a jiya Lahadi.

A sani cewa tantunan da ƴan Najeriya da sauran kasashen Afirka su ke sun fi kilomita uku daga Jamrat.

Tazarar na nufin sai ƴan Najeriya sun yi tafiyar sa’a daya domin yin jifa.

Arabi, ya ce maniyyatan Najeriya za su iya samun tantunan kusa da jamrat amma sai kuɗin aikin hajji ya karu kuma NAHCON ba ta tunanin hakan a halin yanzu.

“Batun samun tantuna a Muna da Arafat kudi ne. Shi ya sa za ka ji koke-koken mutane na biyan makudan kudade don samun tanti.

“ kusan Riyal dubu 20 na Saudiyya ake biya a kama tantunan kusa da Jamrat;