Yadda tawagar HAJJ REPORTERS ta kewaya madafin da ya sarrafa wa jihohin Najeriya 11 abinci a Makkah

0
402

A ranar Laraba tawagar HAJJ REPORTERS ta kewaya madafin Shuraka’a Alkhair kamfanin da ya yi aikin dafa wa wasu jihohin Najeriya 11 abinci yayin aikin Hajjin bana a Makka.

Jihohin da madafin wanda ke aiki ƙarƙashin Al Zumurrud ya dafa wa abinci a Makka sun haɗa da Bauchi, Kaduna, Gombe, Oyo, kebbi, Nasarawa, Ogun, Legas, Osun, Kebbi, Nasarawa, Ondo da kuma Sakkwato.

An kewaya da tawagarmu tare da Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Bauchi, Imam AbdulRahman, sassan madafin. Inda manajan wurin, Bashir Ahmad, ya shaida mana cewa, duk jihar da ke ƙarƙashin kulawarsu ta zo da masu dafa wa alhazanta abinci inda suka yi aiki tare da nasu ma’aikatan domin cim ma buƙatun alhazansu.

Sassa da kuma kayayyakin aikin da aka duba sun haɗa da ɗakin sanyi wanda nan ne akan adana naman kaji da na shanu, da kuma ɗakuna daban-daban inda akan sarrafa namomin da sauran kayan abinci.

Kazalika, an nuna mana ɗakin ajiya inda akan adana sauran kayan abinci kamar su shinkafa da Semovita da Maggi, har ma da kuka wadda aka shigo da ita daga Najeriya da dai sauransu.

Mun samu ganawa da shugabar kicin ɗin mai suna Zainab daga Najeriya wadda suka yi aiki tare da takwarorinta mata su takwas dukkaninsu daga Najeriya.

A cewar Malam Ahmad, suna dafa abinci kimanin 70,000 a kowace rana, kuma baya ga jihohin nan 11 daga Najeriya, suna kuma bai wa alhazan Jamhuriyar Kamaru abinci.

Kazalika, ya shaida wa HAJJ REPORTERS cewa, a bana ba su samu kowane ƙorafi ba daga alhazai sakamakon ɗaukar aikinsu da suka yi da muhimmancin gaske.

Ga wasu sassan bidiyon ziyarar da aka kai: