Mun ware N280bn don bunƙasa wa alhazan Najeriya tantuna a Mina – Kamfanin Saudiyya

0
265

Shugaban Kamfanin Ithraa Alkhair, Dr Ahmad Sindi, ya bayyana cewa, kamfaninsu ya ware kuɗi kusan Dalar Amurka miliyan 200 (kwatankwacin Naira biliyan 280) domin samar da ƙarin tantuna a Mina don amfanin alhazan Najeriya.

Sindi ya bayyana haka ne a wajen wani taron da kamfanin ya shirya inda ya karɓi baƙuncin tawagar Najeriya na Hajjin 2024 ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar Hajji na Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi.

Ya zuwa haɗa wannan rahoton taron na ci gaba da gudana a Crowne Plaza Hotel da ke Jeddah, Saudiyya.

A cewarsa, “Mun rigaya mun ware Riyal Biliyan guda, wato sama da Dala miliyan 200 ($200) domin bunƙasa tantuna a Mina, kuma tare da abokan hulɗarmu, KADINA, muna tattaunawa kan yadda za a samar da ƙarin tantunan,” in ji Dr Sindi.

Da yake ƙarin bayani dangane da Hajjin bana, Dr Sindi ya ce, “Mun shaida aikin Hajjin da aka samu nasara fiye da kowanne a tsakanin shekaru masu yawa saboda ƙwazo da ƙoƙarin da aka nuna.”