Tinubu ya yi ta’zaiyyar rasuwar ɗan jarida, Kabiru Yusuf

0
53

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da ta’zaiyyar rasuwar wani gogaggen ɗan jarida, Kabir Yusuf.

Marigayi Yusuf ya rasu a jiya Talata.

Kafin rasuwar sa, marigayin shi ne wakilin jaridar The Triumph da Radio France a Abuja.

A sanarwar da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Chief Ajuri Ngelale a yau Laraba, Tinubu ya taya iyali da ƴan uwa da abokan arziki na mamacin.

Kafin rasuwar sa, marigayi Yusuf ya kuma zama mai rahoto na musamman a majalisar taraiya.