Hajjin 2024: Yadda muka samar da ƙarin tantuna 12,000 ga alhazan Najeriya a Mina – Kamfanin Saudiyya

0
35

Kamfanin Saudiyya, Ithraa Alkhair wanda ya yi wa alhazan Najeriya aiki a Mina yayin aikin Hajjin da ya gabata a Makka, ya bayyana cewa, ya faɗaɗa ayyukansa yayin aikin Hajjin domin tabbatar da walwalar alhazan.

Wani babban jami’in kamfanin wanda ya buƙaci a sakaya sunansa shi ne ya shaida wa HAJJ REPORTERS hakan yayin zantawarsu a Makka. Inda ya ce, kamfanin ya samu gagarumar nasarar wajen ciyar da aljazai da samar musu da ƙarin tantuna don bunƙasa ayyukan gabanin Hajji tsakaninsa da hukumar NAHCON da kamfanin Mutawiff mai kula da baƙi daga ƙasashen Afirka.

A cewar Jami’in, “Kamfanin Ithraa Al-Khair ya samar da ƙarin wurare yayin aikin Hajjin mai ɗaukar ƙarin alhazai 12,000 a Mina da Arafat wanda hakan ya faɗaɗa rukunin ‘Tents D’ a Mina da kashi 23.

“Wannan ƙarin hidima ne wanda ba ya cikin yarjejeniyar adadin alhazan da aka ware mana son mu yi musu hidima a Mina yayin Hajjin bana. Mun kashe kuɗaɗe masu yawa, amma a shirye muke mu yi dukkan mai yiwuwa domin tabbatar da alhazan sun samu walwala,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Mun samar da wurin shaƙatawa a Arfa a wajen tantunan tare da saka fankoki a kowane layi wanda alhazan sauran ƙasashen ba su samu wannan ba. Wani ƙarin armashin aiki ne da muka samar a bana.”

Kazalika, ya ce da yawan jama’a ba sun da cewa, filo da fankar hannu mai aiki da lantarki da bargo mai kare zafi haɗa da buroshi da man goge bakin da aka samar wa alhazan Najeriya, kamfanin ne ya ɗauki nauyin haka domin gamsar da alhazan.

Daga nan, majiyar tamu ta yaba wa hukumar NAHCON, yana mai cewa, dukkan nasarorin da kamfanin ya samu a bana albarkacin himmar NAHCON ne na tabbatar da alhazan Najeriya sun samu kukawar da ta dace.

“Shugaban kamfaninmu, Dr Ahmed Sindi, ya bayyana mana ƙarara cewa, ba mu da zaɓi face mu ba da himma wajen gamsar da alhazan Najeriya a bana,” in ji jami’in.

Har wa yau, wani jami’in kamfanin na tawagar Injaz wanda ya yi aiki a ƙarƙashin Ithraa Alkhair, shi ma ya yaba wa ƙoƙoƙarin NAHCON yayin aikin Hajjin bana. Wanda a cewarsa, himmar da NAHCON ta nuna yayin Hajjin ta taimaka musu wajen samun nasarori a ayyukansu.

A rahoton farko game da Hajjin 2024 wanda HAJJ REPORTERD ta samu leƙawa, tawagar Injaz ta nuna godiyarta ga jami’an NAHCON bisa haɗin kai da goyon bayan da ta samu daga gare su.