Kungiya Mai Zaman Kanta Da ke Sa Ido da Kawo Rahotanni kan Hajji da Umrah, IHR, ta yi kira ga hukumomin alhazai na jihohi da su fara shirin Hajjin badi da wuri domin samun nasara.
Shugaban IHR na kasa, Alh. Ibrahim Mohammed ne ya yi wannan kira yayin da ya ke jawabi a wajen taron lacca da miƙa lambar yabo na shekara-shekara karo na 15.
A jawabin nasa, Mohamed ya nuna muhimmancin tattali da kuma kiyaye lakoci game da ayyukan Hajji wanda a cewarsa ya kamata hukumomin da alhaki ya rataya a kansu su kula da wannan domin cimma nasara a harkokin Hajji.
Taron wannan karon wanda ya gudana ranar Laraba a babban zauren taron Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, ya maida hankali ne wajen tattauna hanyar da ta dace a bi domin cimma nasara a Hajjin 2025 musamman ta fuskar bai wa lokaci muhimmanci.
A cewar Mohamed, manufar shirya taron shi ne, domin gano kurakuran da aka samu yayin aikin Hajjin da ya gabata da zummar hana aukuwarsu a gaba, da kuma ba da shawarwari kan yadda za a tinkari aikin Hajji mai zuwa.
Ya ce, uk da ƙalubalen da aka fuskanta yayin Hajjin 2024, an samu nasarar jigilar ‘yan Najeriya 58,000 zuwa ƙasar Saudiyya domin sauke farali.
“Wannan adadi kuwa, ya nuna Najeriya ce kan gaba wajen yawan mahajjata daga yankin Afirka, sannan ita ce ta biyar a jerin ƙasashen tasuniya da suka fi yawan alhazai yayin Hajjin da ya gabata”, in ji shi.
Ya ƙara da cewa, nasarorin da Najeriya ta samu yayin Hajjin 2024, hakan ya sa IHR ganin dacewar ta karrama waɗanda suka nuna ƙwazo yayin aikin Hajjin daga farawa har zuwa kammalawa.
Game da Hajjin 2025 kuwa, Mohamed ya ce kwanaki 134 ne suka rage kafin fara shiryawa da kuma raba bisa kamar yadda kalandar Saudiyya dangane da Hajjin 2025 ta nuna.
Haka nan, ya ce, “Ana sa ran rukunin farko na mahajjatan 2025 su isa Saudiyya a ranar 29 ga Afrilun 2025, sannan a yi tsayuwar Arfa a ranar 5 ga Yuni na 2025.”
Sai dai kuma, ya ce abin damuwa ne ainun ganin yadda har yanzu Najeeiya ba ta fara komai dangane da yi wa maniyyata rigista suba da cewa tuni wasu ƙasashen su yi nisa da farawa.
IHR ta kuma yi amfani da wannan dama wajen kira ga Majalisar Dattan Najeriya da a kira taron gaggawa sannan ta hanzarta tantancewa da tabbatar da naɗin sabon shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) domin taimaka wa hukumar kada ta ɓata lolaci wajen fara aiwatar da shirye-shiryen Hajjin 2025.
A nasa ɓangare, Farfesa Wasiu O. Gabadeen wanda shi ne ya gabatar da lacca kan taken taron na bana, ya bayyana muhimmancin kiyaye lokaci musamman a kan abin da ya shafi aikin Hajji. Sannan ya ba da shawararin da yake ganin za su taimaka wajen cimma nasara a Hajjin 2025 muddin aka yi amfani da su.
Yayin taron, an karrama wasu hukumomin alhazai na jihohi da gwamnoni da ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni sufurin jiragen sama da sauransu, saboda ƙwazon da suka nuna yayin Hajjin 2024.
Ga baki ɗaya, Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi ne ya zama gwarzon shekara vame da Hajjin 2024.
Taron ya samu mahalarta daga sassa daban-daban na ƙasar nan da suka haɗa da Gwamnan Jiga da Gwamnan Bauchi da Gwamnan Filato da Ƙaramar Ministar Abuja, jami’an hukumomin Hajji daga Kano, Kaduna, Edo, Legas da sauransu.