Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Adamawa, Malam Abubakar Salihu ya kira wani taron gaggawa da jami’an aikin hajji na kananan hukumomi a jihar.
A wata sanarwa da sashen yaɗa labarai na hukumar ya aikewa Hajji Reporters Hausa, Salihu ya kira taron ne kan tsare-tsaren jadawalin shirye-shiryen aikin Hajjin badi.
A yayin ganawar, Malam Salihu ya yi jawabi a kan batutuwa da dama, inda mafi fice a cikin su shine kudin aikin Hajjin 2025.
A cewar sanarwar, shugaban hukumar ya yi kira ga maniyyata daga jihar da su je banki su fara ajiye Naira miliyan 8.2 na kudin aikin Hajjin kafin hukumar alhazai ta ƙasa ta yanke cikakken farashin aikin hajji na shekara mai zuwa.
Ya kuma umarci jami’an hajji da su fara aikin rijistar maniyyata a kananan hukumomin da su ke aiki.