Farfesa Abdullahi Saleh, shugaban riƙo Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ya yi zaman farko da jami’an hukumar tun bayan naɗa shi da shugaba Bola Tinubu ya yi a kwanan nan.
Farfesa Saleh ya yi taron ne a ranar Juma’a, wanda ya samu halartar jiga-jigan jami’an hukumar.
A jawabinsa na bude taron, shugaban ya mika godiyarsa ga Ubangiji da ya ba shi damar yi wa ƙasa hidima.
Ya kuma lura da damuwa cewa daga cikin bayanan tarukan da su ka gabata a baya, akwai batutuwan da su ka dace da ke bukatar tattaunawa ta gaggawa a kansu.
Farfesa Saleh ya kuma yi addu’ar Allah ya ba sa a yi tattaunawa mai amfani da albarka.
Taron ya samu halartar Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Labarai da Ayyukan Ma’ajiyar Kundaye (PRISLS) Farfesa Abubakar A. Yagawal, Kwamishinan Ayyuka, Gani da Ido da Lasisi, Prince Anofi Elegushi (OIL) ) da Kwamishinan Manufofi, Kula da harkokin ma’aikata da Harkokin kudi (PPMF) Prince Aliu AbdulRazaq. Dr Saleh Usman Muhammad, Mataimakin Shugaban riko na musamman (Bangaren Dabaru).