Hukumar alhzan Yobe ta fara rijistar Hajjin badi tare da karɓar miliyan 8.5 a matsayin kason farko

0
132

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Yobe ta sanar da biyan Naira miliyan 8.5 a matsayin kaso farko na kudin aikin Hajjin badi daga maniyyata.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar ta sanar da cewa ta samu kaso kujerun Hajji 1,288 daga Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON.

Hukumar ta kuma ce nan ba da dadewa ba za ta fara rijistar maniyyatan da ke son zuwa aikin Hajjin 2025 kamar yadda NAHCON ta bayar da shawara.

Shugaban hukumar, Alhaji Mai Aliyu Usman ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Damaturu jim kadan bayan kammala taron gudanarwa da masu karbar kudin aikin hajji na kananan hukumomi 17.

Mai Aliyu Usman ya bayyana cewa NAHCON ta nuna cewa alhazan jihar Yobe za su biya Naira miliyan 8.5 a matsayin biyan farko, inda ya ce za a biya ne gaba daya ko kuma a rarrabe.

A cewarsa, NAHCON ta ware wa jihar kujeru 1,288 domin gudanar da aikin Hajjin 2025, inda daga baya ake jiran karin kaso.

Shugaban zartaswar ya ja hankalin maniyyatan da su fara saka kudadensu daga Naira miliyan 8.5 ko miliyan 7.5 zuwa asusun hukumar.

Ya umurci dukkan jami’an karbar kudaden aikin Hajji na gwamnati su 17 da su gaggauta fara rajistar maniyyata, inda ya shawarci dukkan maniyyatan da su tuntubi masu karbar kudin aikin Hajji a kananan hukumominsu.