Hajj 2025: Maniyyata aikin Hajji a Legas za su fara biyan Naira miliyan 8.5 yayin da aka fara yi musu rajista

0
119

Hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Legas tayi kira da Musulmai a jihar Legas da kewaye wanda ke son zuwa ibadar Aikin Hajji na shekarar 2025 a kasar Saudia da su yanki fom a ofishin ta dake Ikeja daga wannan watan na Satumba.

Sakataren hukumar, Shaheed Onipede ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Taofeek Lawali ya fitar a ranar Laraba.

Acewar Onipede, kudin fom din na aikin Hajji Naira dubu 20 ne, a yayin da maniyyata aikin hajji zasu fara biyan Naira Miliyan 8, 500, 000 kafin sanarwar hukumar kula da aikin Hajji ta kasa kan ainihin abinda za a biya na aikin Hajjin na shekara mai zuwa.

Da yake karin bayani, sakataren hukumar ya ce, “La’akari da yanayin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, hukuma ta yanke shawarar ta mayar da biyan kudin ba kawai lokaci guda ba don bada dama gare su su cimma burin su”.

Yayin da yake kira gare su da kada su biya kudin ga asusu na kashin kai, ya shawarce su da su yi amfani ea asusun hukumar.

Onipede ya bada tabbacin cewa da zarar hukumar NAHCON ta sanya kudin aikin Hajjin kasa da Miliyan 8.5 hukumar zata mayar musu da cikon kudin su.