Gwamnatin Saudiyya ta ci tarar wasu kamfanonin jirgin sama bisa karya dokar lafiya

0
111

Ma’aikatar Lafiya ta Saudi Arebiya ta ci tarar wasu kamfanonin jirgin sama su uku bisa karya dokar kula da lafiya ta ƙasar.

An ci tarar ta su ne bisa dokar cika sharuddan kiyaye lafiya kafin shiga kasar ta sama ko ta ƙasa ko ta ruwa.

Jaridar Saudi Gazette ta rawaito cewa ma’aikatar ta ce an yanke hukuncin ne domin karfafa kiyaye lafiyar al’umma da kuma tabbatar da bin sharudda da dokoki kafin shiga kasar.