Hukumar kula da aikin Hajji ta Ƙasa, NAHCON ta yi bayanin cewa gwamnatin tarayya ba za ta bada tallafin aikin Hajji na 2025 ba.
Tallafin Gwamnatin dai na zuwa ne, bisa tsarin siyar da dala ga Alhazai kan farashi mai sauki daga CBN.
Daily Trust ta rawaito cewa a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar bisa aikin Hajjin 2025, ta ce “Babu tsarin rage kudin canji ga biyan kudin aikin Hajji ga Alhazai dake karkashin jiha ko masu zaman kansu”.
Hakan na nufin idan Dalar Amurka ta ci gaba da zama a Naira 1, 650, kowanne Alhaji zai biya Naira Miliyan 10.
A yayin da har yanzu hukumar NAHCON ba ta sanar da kudin aikin Hajjin na 2025 ba, sai dai wasu jihohin sun sanar da Naira Miliyan 8.5 a matsayin kafin Alkalami.