Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ta ce ta gano yadda wasu ɓatagari ke amfani da sunan ta wajen nemo kwangilar kama masaukai da ciyar da alhazai a Saudi Arebiya.
Hukumar ta kara da cewa waɗannan ɓatagari har ta’addar ta su ta kai su kulla yarjejeniya da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudi Arebiya da sunan NAHCON.
Wata sanarwa da mai magana da yaqin NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar a yau Talata ta ce Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman bai sahalewa wasu kowani ko kamfanoni su ƙulla yarjejeniya da ƙasar Saudiyya don aikin Hajjin 2025 ba.
A cewar sanarwar,, NAHCON na kulla yarjejeniyar ta da gwamnatin Saudiyya ne ta hanyoyin da su ka dace kuma wanda kasar ta saka da su.
“Duk wata yarjejeniya da aka shigar, ba tare da sa hannu da sahalewar shugaban NAHCON ba da kuma shigar ma’aikatan NAHCON kai tsaye cikin harkar to ba sahihiya ba ce,” in ji Usara
Sanarwar ta ce duk mai wani neman sani ko tambayoyi kan aiyukan NAHCON ka iya zuwa kai tsaye domin ƙarin bayani.