Gwamnatin Bangladesh ta yi ragin kuɗin aikin Hajji da kashi 20

0
134

A jiya Laraba ne Gwamnatin Bangladesh ta rage farashin aikin Hajjin badi na 2025 da kashi 20 cikin 100 don saukakawa maniyyata .

A Hajjin da ya gabata, Saudiyya ta bai wa Bangladesh kason kujerar mahajjata dubu127 amma hauhawar farashin kayayyaki da tsadar tikitin jirgi ya sanya maniyyata dubu 85 ne kawai suka iya zuwa aikin Hajjin.

A Hajjin 2024, mafi karancin kudin aikin Hajji na gwamnati ya kusan dala dubu 5, inda a Hajjin 2025 farashin zai ragu da kusan kashi 20 cikin dari.