Ma’aikatar Harkokin Addini, Zakka da Tallafi ta UAE, ta sanar da cewa Saudi Arebiya ta baiwa kasar kason kujerar Hajjin baɗi 60,288.
A cewar jaridar Khaleejtimes, daga cikin wannan kaso, maniyyata 51,732 da su ka yi rijista basu taɓa zuwa aikin Hajji a rayuwar su ba.
A cewar ma’aikatar, an raba kujeru 60,288 da Saudiya ta baiwa ga rabe-raben maniyyata kamar yadda ya ke bisa tsari, ciki har da kujeru 3,051 da aka raba wa masu fama da rashin lafiya da kuma tsofaffi yan shekaru 70 zuwa sama tare da wadanda za su kula da su a yayin aikin Hajjin