Hukumar Alhazai ta Jihar Ogun ta yi kira ga maniyyatan jihar da su gaggauta biyan kaso farko na kuɗin Hajjin baɗi domin samun gurbi da wuri.
Shugaban hukumar, Alhaji Taiwo Ajibola ne ya yi wannan kira a wani taro, inda ya ce duk wand ya fara biya shi za a fara baiwa kujera.