A ranar Litinin ne Iran ta ƙaddamar da fara rijistar Maniyyata aikin Hajjin baɗi a wani dan ƙwarya-ƙwaryar taro.
Wakilin shugaban addini da harkokin Hajji na ƙasar, Hojat-ol-Islam Seyed Abdol Fattah Navab da kuma shugaban hukumar alhazai ta ƙasar, Alireza Bayat ne su ka jagoranci taron.
Bayar ya ce an ƙaddamar da fara kashin farko na yin rijistar ne da wuri akan shekarun baya da su ka gabata don a samu tsaro mai inganci.
Ya ce kuma nan da 15 ga watan gobe na Disamba za a rufe yin rijistar.