Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ta nada Muhammad Ahmad Musa a matsayin sabon kakakin ta.
HAJJ REPORTERS ta lura da sauyin da aka samu a bangaren yaɗa labarai bayan fitar da wata sanarwar akan mayar da kudaden Hajjin 2023 ga alhazai.
Muhammad Ahmad Musa ne ya sanya hannu a sanarwar, wanda a yanzu ke rike da mukamin shugaban hulda da jama’a na hukumar.
Wani bincike da HAJJ REPORTERS ta yi ya nuna cewa Muhammad Ahmad Musa ya karbi mukamin ne, inda ya maye gurbin Hajiya Fatima Sanda Usara da ke rike da shi a baya.